logo

HAUSA

Shugaban kasar Micronesia zai ziyarci kasar Sin

2024-04-03 20:07:33 CMG Hausa

 

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce bisa gayyatar shugaban kasar Sin Xi Jinping, shugaban kasar Micronesia Wesley W. Simina, zai ziyarci kasar Sin, tsakanin ranaikun 5 zuwa 12 ga watan nan na Afirilu.

Kaza lika, yayin taron manema labarai na Larabar nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce wannan ne karon farko da shugaba Simina zai ziyarci kasar Sin tun bayan kama aikinsa a matsayin shugaban kasa. Wang ya ce yayin ziyarar aikin, ana sa ran shugabannin kasashen biyu za su zurfafa musayar ra’ayoyi, don gane da bunkasa alakar dake tsakanin kasashensu, da sauran batutuwa masu nasaba da moriyarsu.

Jami’in ya kara da cewa, Sin a shirye take ta yi aiki da Micronesia, wajen mayar da wannan ziyara a matsayin damar bunkasa amincewa juna ta fuskar siyasa, da zurfafa hadin gwiwa ta zahiri, da fadada musaya tsakanin al’ummun sassan biyu, da ma ingiza huldar dake tsakanin Sin da Micronesia.   (Saminu Alhassan)