logo

HAUSA

Sin Ta Musanta Rahoton Amurka Game Da Harkokin Cinikayya

2024-04-03 21:19:38 CMG Hausa

Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ta musanta rahoton da kasar Amurka ta fitar mai zargin Sin din da kafa shingayen cinikayyar waje. Wata sanarwa da kakakin ma’aikatar ya fitar a jiya Talata, ta ce Sin na adawa da yadda Amurka ta ayyana ta a matsayin “kasa da ake nuna damuwa kanta”.

A ranar 29 ga watan Maris da ya shude ne Amurka ta fitar da rahoton kasa, na kiyasta hada-hadar cinikayya mai nasaba da shingayen cinikin waje, wanda a cikinsa, Amurkan ta yi zargin cewa, wai "akwai hujjoji isassu dake nuna Sin na aiwatar da manufofi, da matakai da suka sabawa dokokin kungiyar cinikayya ta duniya WTO. Har ila yau, rahoton ya zargi Sin da aiwatar da wasu matakai da suka sabawa yanayin kasuwa, da sanya wasu shingaye kan albarkatun gona, da ma manufofin tattara bayanai.

Kakakin ya kara da cewa, tun bayan da ta shiga WTO, Sin ta ci gaba da tallafawa tsarin cinikayya na sassa daban daban, ta rika fadada bude kofarta ga dukkanin sassa, tare da samar da tsari mai gamsarwa na kasuwa da shari’a, wanda ya samu karbuwa matuka tsakanin sassan kasa da kasa.

Bugu da kari, sanarwar ta yi kira ga Amurka, da ta dakatar da zargi maras hujja kan sauran kasashe, ta kuma rungumi dokokin WTO, da ka’idojin adalci da daidaito na cinikayyar kasa da kasa.  (Saminu Alhassan)