logo

HAUSA

Gwamnan jihar Zamfara ya nemi agajin shugaban tarayyar Najeriya wajen kawo karshen ayyukan `yan ta`adda a jihar

2024-04-02 11:02:24 CMG Hausa

Gwamnan jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya Alhaji Dauda Lawan ya nemi agajin gwamnatin tarayya wajen kawo karshen ayyukan `yan ta`adda a jihar.

Gwamnan ya bukaci hakan ne lokacin da ya ziyarci shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa dake Abuja, ya ce bukatar agajin ya zama wajibi saboda yadda ayyukan `yan ta`addan ke cigaba da yin munmunan tasiri a jihar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A lokacin da yake zantawa da `yan jaridun dake fadar shugaban kasa, gwamnan na jihar ta Zamfara Alhaji Dauda Lawan ya ce duk da kokarin da gwamnatin jihar ke yi wajen yakar `yan ta`addar, amma har yanzu yanayin tsaro a jihar sai ci gaba yake yi da tabarbarewa.

Ya ci gaba da bayanin cewa irin wannan yanayi da al`ummar jihar ke cikin ne ya sanya shi ziyartar shugaban kasar, domin ya yi masa bayani tare da nema agajin gwamnatin tarayya, saboda ita ce ke da sojoji da sauran hukumomin tsaro.

Gwamnan na jihar Zamfara ya ce ya nemi a samar da Karin sojoji a jihar tare da ba su kayan aiki wadatattu, ta yadda za su yi aikin da ya kamata domin fatattakar `yan ta`addar da nufin tabbatar da samun dauwamammen zaman lafiya a jihar baki daya.

Ya ci gaba da bayanin cewa yanzu jihar ta Zamfara ta kasance matattarar `yan ta`adda, kuma muddin aka yi sakacin yi wa tufkar hanci, lamarin zai iya shafar daukacin arewacin Najeriya.

“Yanayin tsaro a Zamfara ya dauki wani salo na daban, musamman ma a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, an kai hare-hare da dama ga al`ummomin wasu kananan hukumomi, a don haka a matsayin na gwamna na ga dacewar na sanar da shugaban kasa, kuma ya gamsu sosai da bayanan da na yi masa, inda ya ba ni tabbacin cewa za a yi wani abu mai karfi cikin gaggawa domin shawo kan lamarin”(Garba Abdullahi Bagwai)