logo

HAUSA

Ana gudanar da babban taron fasahohin nuna bayanai na kasa da kasa na 2024

2024-04-02 14:32:05 CMG Hausa

An bude babban taron fasahohin nuna bayanai na kasa da kasa na 2024 a birnin Hefei dake lardin Anhui daga ranar 31 ga watan Maris, inda zai gudana har zuwa 3 ga watan Afrilu. Kwararru da masana gami da kamfanoni daga bangaren raya fasahohin nuna bayanai na kasashe da yankuna 19 suna taruwa, don more fasahohion zamani tare, da tattaunawa kan ci gaban masana’antun, ta yadda za a sanya sabon kuzari ga masana’antun fasahohin nuna bayanai.

Jigon wannan babban taron shi ne “Hasashen ci gaban masana’antun nuna bayanai”, wanda ke kunshe da rahotannin fasahohi sama da dari 7 da aka gabatar, da muhimmin jawabin da aka gabatar a bikin bude taron, gami da sauran wasu tarukan koli masu jan hankalin al’umma.

Kamfanonin kasa da kasa fiye da 90 da suka shafi fannoni daban daban kamar samar da kayayyaki, sassan na’urori, na’urorin tattara bayanai na chip, da kayayyakin aiki da sauransu, sun kawo fasahohi da kayayyakin nuna bayanai na zamani.

Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya nuna kayayyakin samar da shirye-shirye na HD da ya kera tare da kamfanonin Sin, wadanda suka hada da kyamarar 8K, na’urorin VCR , allunan kallo wato Screen, da tsarin musayar siginar IP da saruransu, dukkansu sun nuna fasahar samar da shirye-shirye mai cikakken tsarin HD.(Safiyah Ma)