logo

HAUSA

An nada Judith Tuluka Suminwa a matsayin sabuwar firaministan DRC

2024-04-02 09:55:43 CMG Hausa

Ofishin shugaban kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, ya sanar da nadin Judith Tuluka Suminwa, a matsayin sabuwar firaministan kasar.

Judith Tuluka Suminwa, wadda ta taba rike mukamin ministar tsare-tsare, ta shiga kundin tarihi, inda ta zama mace ta farko da za ta rike mukamin firaminista a kasar.

Sabuwar firaministan mamba ce ta jamm’iyyar Union for Democracy and Social Progress mai mulkin kasar, wadda ta lashe kujeru 69 daga cikin 500 na majalisar dokokin kasar, lamarin da ya ba ta damar zama jagora cikin sauran jam’iyyun kasar 44, yayin babban zaben kasar da aka yi a watan Disamban shekarar 2023. (Fa’iza Mustapha)