logo

HAUSA

Hukumar tsaro ta Civil Depence a tarayyar Najeriya ta sake bankado haramtattun matatun mai a jihar Rivers

2024-04-01 09:38:39 CMG Hausa

Hukumar tsaron fararen hula ta Civil Depence a tarayyar Najeriya ta tabbatar da lalata haramtattun matatun mai 10 a wani daji dake yankin karamar hukumar Etche a jihar Rivers ta kudancin kasar.

Yayin wani samame da dakarun musamman na hukumar masu yaki da barayin mai suka kai dajin, sun samu nasarar kame mutane biyar tare da lalata rumbunan ajiyar danyen mai da aka gina guda 50.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kamar yadda ya shaidawa manema labarai yayin wannan samame, kwamandan hukumar mai lura da jihar Rivers Mr. Basil Igwe-bueze ya ce dakarun hukumar sun kuma bankado wani bututun mai da aka binne wanda barayin man ke amfani da shi wajen dakon danyen mai kai tsaye daga rijiyoyi zuwa haramtattun matatun man da suka samar.

Ya ce sun samu nasarar gano wadannan wurare ne ta hanyar sahihan bayanan sirri da suka samu wanda hakan ya kai ga kame wasu daga cikin barayin tare da na`urorin da suke amfani da su.

“Duk wani abu da yake da nasaba da satar mai da hakar ma`adanai ta haramtattun hanyoyi, da ma sauran ayyukan da za su iya haifar da zagon kasa ga harkokin tattalin arzikin kasa za mu rinka daukar sa da mahimmancin gaske, sabo da hukumar Civil Depence a yanzu ita ce a kan gaba wajen yaki da satar danyen mai tare da kare muhimman kayayyaki da kadarorin gwamnati a kasa”

Hukumar ta tabbatar da cewa tuni ta fara gudanar da bincike domin gano wadanda suke da hannu wajen daure gindin samar da wadannan haramtattun matatun mai, kuma ba za a saurara masu ba wajen zartar da hukuncin da ya dace a kan su domin ya zama izina ga sauran jama`a.(Garba Abdullahi Bagwai)