logo

HAUSA

Kasar Sin ta samu ci gaba mai inganci a manyan bangarori 5

2024-04-01 10:28:55 CMG Hausa

Kasar Sin ta samu gagarumin ci gaban tattalin arziki da zamantakewa, musammam a manyan bangarori 5 da suka hada da walwalar jama’a da sayayya da samar da kayayyaki da ababen more rayuwa da bangaren bayar hidimomi.

Wani rahoto da cibiyar nazarin hada-hadar kudi ta Chongyang dake jami’ar Renmin ta kasar Sin da wasu cibiyoyin bincike na gama kai daga Amurka da Rasha da Canada da India suka fitar jiya Lahadi, ya bayyana irin ribar da Sin ta samu daga ci gabanta, inda suka kwatanta shi da taruwar ribar kudin ruwa daga ajiya na tsawon lokaci.

A cewar rahoton, ci gaba da zamanantar da kasar Sin, ka iya kawo karin ci gaba ga kasar, lamarin da zai kasance wani karfi da zai ingiza ci gaban tattalin arziki mai dorewa da samar da wadata a kasar. Haka kuma, sun bayyana cewa, karuwar ci gaban kasar Sin, ta samo asali ne daga dorewar kudin shigar da take samu a mataki mai karko, cikin lokaci mai tsawo.

Har ila yau, rahoton ya kara da cewa, kuzarin zamanantar da kasar Sin, wanda ya dogara da ci gaban kasar, na mayar da hankali ne kan shirye-shiryen kirkire-kirkire da zurfafa gyare-gyare a gida da fadada bude kofa ga kasashen waje da inganta samun ci gaba ta hanyar kare muhalli. (Fa’iza Mustapha)