logo

HAUSA

Yan gudun hijirar Najeriya fiye da 1400 suka shiga yankin Maradi mai iyaka da Najeriya

2024-04-01 14:17:19 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, kasa da mako guda, fiye da mutane 1400 suka yi gudun tashe-tashen hankali na kungiyoyi masu dauke da makamai, zuwa kauyukan yankin Maradi, mai iyaka da Najeriya.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da rahoto

Shi dai wannan gudun hijira na al’umma, na kasancewa mafi girma tun farkon sabuwar shekarar 2024.

Yawancin wadanda suka gudu mata ne da yara kanana, kuma wadannan mutane 1400 sun warwatsu zuwa wurare uku na yankin Maradi, a karshen makon da ya gabata, dalilin tashe tashen hankalin da ya barke tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai da kungiyoyin ‘yan banga a ‘yan kwanakin da suka wuce cikin jahar Sokoton Najeriya. Tun zuwansu a kasar Nijar, kungiyoyin jin kai suka fara fadi katashin bada taimakon gaggawa ga wadannan mutane.

Christelle Hure, shugabar reshen kula da taimako a yammaci da tsakiyar Afrika, ta bayyana cewa wadannan mutane ba su zo da kome ba, ba su da abinci kuma ba su da takardun kasa.

A dunkule, suna bukatar abinci, matsuguni, kiwon lafiya da ruwan sha cikin gaggawa, in ji wannan jami’ar, tare da bayyana cewa zuwan wadannan sabbin ‘yan gudun hijira, wani babban kalubale wajen kula da albarkatun al’umomin wurin, da su ma suke da rauni.

A nasa bangare, babban kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta HCR, ya bayyana cewa an fara sake tsugunar da wadannan mutane, musammun ma a kauyen Chadakori.

A watan da ya gabata, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta yi rejistan ‘yan gudun hijiran Najeriya fiye da dubu 62 da ke yankin Maradi na kasar Nijar.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.