logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na Indonesia

2024-04-01 20:19:11 CMG Hausa

A yau Litinin 1 ga watan Afrilu ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na kasar Indonesia Prabowo Subianto, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing.

A yayin shawarwarin da suka gudanar, shugaba Xi Jinping ya taya Prabowo murnar zama sabon shugaban kasar Indonesia. Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata Sin da Indonesia su bi hanyar samun ci gaba dake dacewa da yanayinsu, da nuna goyon baya ga juna kan tabbatar da ikon mallakan kasa, da tsaro, da moriyar bunkasuwa, da kuma manyan batutuwan dake shafar moriyarsu.

Xi Jinping ya ce, Sin tana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Indonesia a dukkan fannoni, da raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Indonesia, wadda za ta yi babban tasiri ga yankin da ma duniya, ta yadda jama’ar kasashen biyu za su kara amfana, da kuma samar da gudummawar shimfida zaman lafiya, da zaman karko, da wadata a yankin, da duniya baki daya.

A nasa bangare, Prabowo ya ce, yana farin ciki da ziyararsa a kasar Sin, a matsayin kasa ta farko da ya ziyarta, tun bayan ya hawa kujerar shugabancin Indonesia. Ya ce, kasar Sin muhimmiyar abokiya ce ga kasarsa ta fuskar hadin gwiwa. Ya kuma bayyana goyon bayansa ga raya dangantaka tsakanin kasashen biyu, da tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, da sa kaimi ga raya dangantaka mai inganci a dukkan fannoni a tsakaninsu, don raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Indonesia. (Zainab Zhang)