logo

HAUSA

Somalia ta karbi riga kafin Kwalara miliyan 1.4 yayin da ake samun karuwar masu kamuwa da cutar

2024-04-01 10:42:32 CMG Hausa

Kasar Somalia ta karbi riga kafin cutar Kwalara na digo guda miliyan 1.4 da darajarsu ta kai dala miliyan 2.5, daga Asusun Kula da Kananan Yara na MDD (UNICEF), yayin da ake samun karuwar wadanda ke kamuwa da cutar a kasar.

Wata sanarwa da asusun UNICEF ya fitar da yammacin jiya Lahadi a Mogadishu, ta ruwaito cewa za a raba riga kafin ne ga gundumomi 5 da cutar ta fi shafa a fadin kasar, a wani yunkuri na gaggauta dakile bazuwarta. Ta kara da cewa, tun daga watan Janairu, mutane 4,388 sun kamu da cutar, yayin da ta yi sanadin rayuka 54, da 2 bisa 3n adadin yara ne.

A cewar sanarwar, baya ga riga kafi da magunguna, asusun UNICEF da abokan huldarsa za su matsa kaimi wajen inganta hidimomin da suka shafi samar da ruwa da tsaftar muhalli da jiki a yankunan da cutar ta shafa da kuma wayar da kan al’ummomi kan matakan kariya. (Fa’iza Mustapha)