logo

HAUSA

Sin Da Faransa Sun Amince Da Gina Alaka Bisa Daidaito Da Hangen Nesa

2024-04-01 19:51:31 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce kasarsa da kasar Faransa, sun amince su kara bunkasa tattaunawa, da tsare-tsaren aiki, da musaya, da hadin gwiwa, ta yadda za su kai ga gina alaka mai kunshe da karin daidaito da hangen nesa bisa manyan tsare-tsare.

Wang ya bayyana hakan ne a Litinin din nan, yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da takwaransa na Faran Stephane Sejourne, bayan sun kammala ganawa a nan birnin Beijing.

Mista Wang ya shaidawa manema labarai cewa, a matsayin Sin da Faransa na kasashe masu bin tsarukan kai su, ya dace su taka rawar gani wajen bunkasa goyon baya tsakanin sassan kasa da kasa, su raya kirkire-kirkire da wanzar da ci gaba. Kaza lika, kamata ya yi kasashen biyu su rungumi aiwatar da manufofi a fayyace, da cimma moriyar juna, da tattaunawa tsakanin mabambantan wayewar kai.

Yayin zantawar manyan jami’an biyu, Wang Yi ya bukaci bangaren Faransa da ya dora muhimmancin gaske, wajen shawo kan damuwar kasar Sin don gane da hakkokinta, ya kuma samar da yanayin gudanar da kasuwanci mai kyau bisa adalci, maras nuna wariya ga kamfanonin kasar Sin.

Ya ce, ya dace Sin da Faransa su kasance masu murya guda, kan batutuwan da suka shafi wanzar da zaman lafiya da daidaito a duniya, su ingiza makomar bil Adama, da goyon bayan juna wajen aiwatar da kudurorin tabbatar da tasirin sassa daban daban. (Saminu Alhassan)