logo

HAUSA

Sin Na Maraba Da Ziyarar Mai Rikon Mukamin Magajin Garin Birnin San Francisco

2024-04-01 20:25:43 CMG Hausa

A yau Litinin ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi maraba da ziyarar da mai rikon mukamin magajin garin birnin San Francisco na kasar Amurka London Breed za ta kawo kasar Sin a mako mai zuwa.

Bisa tsarin ziyarar, London Breed za ta baro gida a ranar 13 ga watan nan na Afrilu, inda za ta ziyarci yankin musamman na Hong Kong, da biranen Shenzhen, da Guangzhou, da Beijing da kuma Shanghai, wanda shi ne birnin kawance da San Francisco.

Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana fatan cewa, ziyarar ta Breed za ta haifar da babbar nasara, kana za ta kara ingiza hadin gwiwar birnin San Francisco da kasar Sin, da ma musaya tsakanin yankunan Sin da na Amurka.

Wang Wenbin, ya ce har kullum kasar Sin na goyon baya, tana kuma karfafa gwiwar al’ummu daga dukkanin sassan rayuwa na kasashen biyu da su yaukaka cudanya, da musaya, da cimma matsaya, da kara amincewa juna. Kana su kauracewa tsoma hannu cikin harkokin da ba nasu ba. Su kuma zurfafa hadin gwiwa don janyowa al’ummunsu karin alherai. (Saminu Alhassan)