logo

HAUSA

Zargin da Philiphines ta yi kan kasar Sin ba bisa gaskiya ba ne

2024-04-01 17:20:47 CGTN HAUSA

 

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya mai da martani kan zargin da Philipines ta yi wa kasar Sin game da batun tekun kudancin kasar Sin, inda ya ce, Philiphines ta yi haka ne da nufin boye gaskiyar cin amanar alkawarin da ta yi kan batun tare da keta hakkin kasar Sin.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, ma’aikatar tsaron kasar Philiphines ta ba da sanarwa kwanan baya cewa, sanarwar da Sin ta bayar kan batun kudancin kasar Sin a ‘yan kwanakin da suka wuce, ta nuna cewa, gwamnatin kasar tana nuna girman kai da cin zalin na kasa da ita.

A gun taron manema labarai da aka yi a yau Litinin, Wang Wenbin ya amsa tambayar da aka yi masa game da wannan batu, inda ya ce tsibiran Nansha ciki hadda sashen tudun ruwa na Ren’ai Jiao, yankunan kasar Sin ne tun fil azal. Kuma zargin da kullum Philiphines take yi kan kasar Sin ba bisa gaskiya ba ne, tana nufin mai da fari baki, don gudun zargin da aka yi mata kan cin amanar alkawarin da ta yi da keta hakkin Sin kan batun tekun kudancin kasar ta Sin.

Yayin da aka tabo maganar kayyade takardar iznin shiga Amurka kan jami’an yankin Hongkong, Wang ya ce, Sin za ta mai da martani mai tsanani a kai. (Amina Xu)