logo

HAUSA

Alkaluman PMI Na Sin Sun Koma Kan Turbar Bunkasa

2024-03-31 16:23:02 CMG Hausa

Alkaluman PMI sun kai ga maki 50.8 a watan nan na Maris a kasar Sin, wanda hakan ke nuni ga yadda mizaninsu ya hau turbar bunkasa.

Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS ta fitar a Lahadin nan sun fayyace cewa, makin PMI sama da 50 na nuna bunkasar fanni, yayin da kasa da maki 50 ke nuna koma-baya.

Alkaluman PMI na Sin sun juya zuwa mizanin bunkasa bayan watanni 5 a jere na koma-baya da suka fuskanta, tun daga watan Oktoban shekarar 2023, wanda hakan ke nuni ga farfadowar hada-hadar kere-kere na kasar Sin.

Babban jami’in kididdiga na hukumar NBS Zhao Qinghe, ya ce sassa 15 ciki 21 da aka nazarci PMI din su, sun kara bunkasa a watan na Maris, adadin da ya dara na watan da ya gabata mai sassa 10, a gabar da kamfanoni ke ta fadada ayyukansu bayan wucewar hutun bikin Bazara na bana.

Har ila yau, alkaluman da aka fitar a yau sun nuna cewa, sassan PMI da ba na kere-kere ba sun daga zuwa maki 53 a watan na Maris, sama da maki 51.4 da suke a watan Fabrairu.

Wannan dai karuwa ta baya-bayan nan na nuna fadadar mizanin sassan da ba na kere-kere ba, musamman a watannin baya-bayan nan, wanda hakan ke kara shaida dawowa, da bunkasar hada-hadar fannonin da ba na kere-kere ba a kasar Sin.   (Saminu Alhassan)