logo

HAUSA

An bude sabon shafin internet na samar da hidimomi na kasa da kasa na Beijing

2024-03-31 16:38:39 CMG Hausa

An bude sabon shafin internet na samar da hidimomi na kasa da kasa na Beijing, wato International Web Portal of Beijing a hukumance, wanda zai rika samar da hidimomi, kamar na gabatar da sakwanni, da hidimar zamantakewar al’umma, da amsa tambayoyi da sauransu, a kokarin raya Beijing ta zama cibiyar mu’amala tsakanin kasa da kasa.

Shafin wanda aka kaddamar a kwanan baya, ya tanadi hidimomi a harsuna 9, wato Turanci, da harshen Koriya, da Japananci, da harsunan Jamus, da na Sifaniya, da Rasha, da Potugal da Faransanci, da Larabci.

An bude wannan sabon shafi ne domin samar da hidimomi, da gwada ayyukan da ake gudanarwa ga jama’a da masu zuba jari na kasashen ketare a fannonin biyan kudi, da sufuri, da karatu, da zaman yau da kullum, da yawon shakatawa da sauransu.

Haka zalika kuma, bisa abubuwan dake shafar yanayin ciniki na Beijing da dai sauransu, a kan sabon shafin an gabatar da sakwanni, da abubuwa masu nasaba da samun bunkasuwar tattalin arziki, da fifikon zuba jari, da manyan sha’anoni na yankunan da sauransu, don samar da hidimomin jawo jari, da amsa tambayoyi game da zuba jari daga kamfanonin ketare dake birnin Beijing. (Zainab Zhang)