logo

HAUSA

Za a dauki nauyin karatun dalibai 137 da aka ceto daga hannun ’yan bindiga a jihar Kaduna ta arewacin Najeriya

2024-03-31 16:53:32 CMG Hausa

Gwamnan jihar Kaduna dake arewacin Najeriya Sanata Uba Sani ya yi alkawarin daukar nauyin karatun dalibai 137 da aka ceto kwanan nan daga hannun ’yan bindiga bayan sace su da aka yi a makarantar sakandare da ta firamaren garin Kuriga dake jihar.

Gwamnan ya tabbatar da hakan ne lokacin da yake mika daliban ga iyayen su bayan jami’an tsaro sun samu nasarar kwato su, haka kuma gwamnan ya bayar da kyautar naira miliyan 10 ga iyalan malamin da ya mutu a hannun ’yan bindigar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Gwmanan na jihar Kaduna ya yaba bisa kokarin jami’an tsaron wajen ceto daliban bayan sun shafe kwanaki 16 a hannun ’yan bindigar, ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta sake kawata harabobin makarantun biyu tare da samar da managartan matakan tsaro a dukkannin makarantun dake jihar ta Kaduna.

Sanata Uba Sani ya ci gaba da cewa, kafin gwamnati ta damka daliban ga iyayen su, sai da aka tanadi rukunin likitoci da suka duba yanayin koshin lafiyar su.

“Kamar yadda na alkawaranta, wadannan yara za su cigaba da kasancewa ’ya’ya na, kuma zai yi amfani da gidauniya ta wato Uba Sani Foundation wajen tallafawa karatun su.”

Gwamnan na jihar ta Kaduna ya tabbatar da cewa, babu ko da sisin kwabo da aka baiwa ’yan bindigar kafin yaran su sami ’yanci.

Tun dai a ranar Alhamis da ta gabata ne, daliban suka sadu da iyayen su bayan ganawar da suka yi da jami’an gwamnatin jihar ta Kaduna.(Garba Abdullahi Bagwai)