logo

HAUSA

Sin da EU sun gudanar da taron tattaunawa domin inganta musaya tsakanin jama’arsu

2024-03-30 16:49:15 CMG Hausa

An gudanar da taron tattaunawa tsakanin manyan jami’an kasar Sin da Tarayyar Turai EU a jiya Jumma’a a birnin Beijing, inda bangarorin biyu suka amince da kara inganta musaya tsakanin jama’arsu da kuma aiwatar da hadin gwiwa a aikace.

Yayin taron wanda aka yi jiya Juma’a a birnin Beijing, ‘yar majalisar gudanarwar kasar Sin Shen Yiqin, ta tattauna da Iliana Ivanova, kwamishinar kula da kirkire-kirkire da bincike da al’adu da ilimi da matasa na Tarayyar Turai.

Bangarorin biyu sun tattauna game da muhimmiyar rawar da ilimi zai taka wajen inganta komawa ga tsarin rayuwa mai kiyaye muhalli da bukatar da ake da ita ta samar da daidaito wajen zirga zirgar dalibai ba tare da matsala ba, wanda ya samu koma baya sosai yayin annobar COVID-19. Taken tattaunawar na bana shi ne, “Hada hannu domin samun ingantaccen muhalli da makoma mai dorewa”

Sin da EU sun dawo da musaya da tattaunawa a tsakaninsu a dukkan matakai ne tun bayan annobar COVID-19. Zuwa Nuwamban 2022, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da shugaban Faransa Emmanuel Macro da sauran shugabannin nahiyar Turai, sun ziyarci kasar Sin daya bayan daya. Haka zalika, kasar Sin ta fara bayar da damar shigowa kasar ba tare da shaidar Visa ba ga karin kasashen Turai da suka hada da Faransa da Jamus da Italiya da Switzerland da Ireland da Austria da Belgium. (Fa’iza Mustapha)