logo

HAUSA

Damarmaki suna kasar Sin

2024-03-30 16:50:25 CMG Hausa

An rufe taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa tsakanin kasashen Asiya na Boao na tsawon kwanaki hudu da maraicen jiya Jumma’a 29 ga wata a birnin Boao na lardin Hainan na kasar Sin. Taron ya samu halartar wakilai daga fagen siyasa da na bangarorin masana’antu da kasuwanci da kwararru da masana kusan dubu 2 daga kasashe da yankuna sama da 60. Mahalarta taron da dama sun ce, ba karfin dorewa da makoma mai haske kadai tattalin arzikin kasar Sin ke da su ba, har ma yana kunshe da wasu sabbin fannonin ci gaba. Tsohon firaministan kasar Japan, Yukio Hatoyama yana ganin cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da bunkasa yadda ya kamata, wanda zai haifar da babban tasiri ga duk duniya.

A yayin taron kuma, “karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko” shi ma ya ja hankali sosai. Da yake tsokaci, jakadan kasar Turkiyya dake kasar Sin, İsmail Hakkı Musa, cewa ya yi, hakan na nufin cewa, Sin a shirye take don raya sabon salon habaka tattalin arziki, da zummar shawo kan kalubalen duniya, da kirkiro makoma mai haske.

Kaza lika, samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba da kasar Sin take yi, shi ma ya burge mahalarta taron. Alkaluman sun ce, kawo yanzu kasar Sin ta riga ta samu gagarumin ci gaba a fannonin da suka shafi gine-gine masu kiyaye muhalli, da makamashi mai tsafta, da kuma gudanar da salon rayuwa ba tare da gurbata muhalli ba.

Bugu da kari, ba za’a iya raba samar da ci gaba tare da manufar bude kofa ga kasashen waje ba. A kwanan nan ne, kasar Sin ta bullo da wasu jerin matakai na fadada bude kofarta ga kasashen waje, ciki har da ci gaba da rage sassan da a baya aka takaitawa baki ‘yan kasashen waje zuba jari.

A kasar Sin, ana iya ganin wata makoma mai haske, wato yin kirkire-kirkire, da kiyaye muhalli, da bude kofa ga kasashen waje, da kuma more damarmaki tare da sauran kasashe. (Murtala Zhang)