logo

HAUSA

Me ya sa masu amfani da yanar gizo ta Intanet a Amurka suka yi wa Janet Yellen dariya kan kalamanta masu ban mamaki?

2024-03-30 15:27:54 CMG Hausa

Yayin da take ziyara a wata masana’antar kera batir bisa karfin hasken rana dake jihar Georgia a kasar Amurka kwanan nan, sakatariyar kudin kasar, Janet L. Yellen, ta bayyana cewa, sana’ar bunkasa sabbin makamashi ta kasar Sin na fuskantar matsala, wato yawan hajojin da ake samarwa ya wuce yawan bukatun da ake da su, al’amarin da ya jirkita farashin kayayyaki gami da salon samar da su a duk duniya, tare kuma da kawo illa ga muradun kamfanoni gami da ma’aikatan kasar ta Amurka. Game da wannan batu, Yellen ta ce za ta dauki matakan kare kamfanoni gami da ma’aikatan Amurka, don su shiga takara cikin wani dandali “mai adalci”.

Irin wadannan kalamai na Janet Yellen sun janyo dariya daga masu amfani da yanar gizo ta Intanet a Amurka, inda suka ce, tun farko Yellen ta ce kasar Sin ta gaza a fannin raya makamashi mai tsafta, amma yanzu ta fara zargin kasar da cewa ta wuce gona da iri. To, me ya sa Amurka ba za ta iya yin shiru, ta yi harkar gabanta ba? Wasu kuma sun ce, da Amurka tana da fifiko a fagen takara, to za ta ce a raya kasuwa marar shinge, amma tun da ba ta da shi, za ta koma ga ra’ayin bada kariya ga harkokin cinikayya. Ke nan wannan ita ce ka’idar Amurka.

A shekara ta 2023, jimillar darajar wasu sabbin hajoji uku kirar kasar Sin da aka fitar zuwa kasashen ketare ta zarce kudin kasar wato Yuan tiriliyan 1.06, ciki har da motoci masu amfani da makamashin wutar lantarki, da batir irin na lithium-ions, gami da batir mai amfani da makamashin hasken rana. Ba karfin tattalin arzikin da kasar Sin ke da shi kawai wannan abun ya nuna ba, har da taimakawa sauran kasashe komawa kan raya makamashi mai tsafta, al’amarin da ya bayar da babbar gudummawa ga tinkarar sauyin yanayin dake addabar duniya.

Amma a ra’ayin wasu ‘yan siyasar Amurka, sabbin sana’o’in kasar Sin na bunkasa cikin sauri, abun dake illata moriyarsu. To, yaya za su yi? Abun da suka yi ba kyautata fasahohi don inganta karfinsu na yin takara ba ne, suna yunkurin shafawa kasar Sin bakin fenti, da kawo cikas, da keta hakkin al’ummar kasar na samar da ci gaba, bisa hujjojin “tsaron kasa”, ko kuma “yawan hajojin da ake samarwa ya wuce yawan bukatun da ake da su”.

Wasu kwararru na kungiyar masana ta Brookings Institution dake Amurka na ganin cewa, hadin-gwiwar Sin da Amurka da ta shafi fasahohin makamashi mai tsafta, ka iya taimaka musu wajen rage fitar da iska mai gurbata muhalli, da kara samun fahimtar juna a tsakaninsu. Kaza lika, sun ce, idan kuma aka maida wannan bangaren a matsayin wani filin yin takara na daban, za’a kawo babbar illa ga aikin samar da kayayyaki a duk duniya gami da ajandar tinkarar sauyin yanayi. (Murtala Zhang)