logo

HAUSA

Shugabancin JKS ya nazarci rahoton rangadin tabbatar da da’a

2024-03-29 21:53:02 CMG Hausa

Ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya gudanar da taro a yau Juma’a domin nazartar cikakken rahoton ayyukan rangadin tabbatar da da’a zagaye na biyu, na kwamitin kolin karo na 20.

Sakatare janar na kwamitin kolin JKS, Xi Jinping ne ya jagoranci taron.

An bayyana yayin taron cewa, ayyukan rangadin tabbatar da da’a da aka yi sau biyu bayan gudanar da taron wakilan jam’iyyar na kasa karo na 20, ya shafi dukkan kamfanoni mallakar gwamnati

Taron ya bayyana cewa, an karfafa gina tsarin jam’iyyar a dukkan kamfanonin mallakar gwamnati da ma sassa masu ruwa da tsaki, da samun sabbin nasarori ta fuskar tafiyar da jam’iyyar. (Fa’iza Mustapha)