logo

HAUSA

Karamar jakadiyar Sin a Najeriya ta ziyarci wasu kauyuka don nazarin aikin taimakawa kauyukan Afirka samun damar kallon talabijin

2024-03-29 12:34:35 CMG Hausa

Karamar jakadiyar Sin dake karamin ofishin jakadancin Sin na jihar Lagos dake kudancin Najeriya Yan Yuqing, ta ziyarci wasu kauyuka na jihar Lagos, da suka hada da Orimedu, da Sangotedo, domin nazarin yadda ake tafiyar da aikin taimakawa mazauna wurin wajen samun damar kallon talabijin. 

Yayin ziyarar ta Yan, ta leka wasu makarantun sakandare, da gidajen al’ummun wurin, don gane yadda aikin ke amfanar da su, kana ta mika gaisuwarta ga malamai, da dalibai da kuma mazauna kauyukan.

Jakadiya Yan ta bayyana wa mazauna wurin cewa, aikin taimakawa mazauna kauyukan kasashen Afirka samun damar kallon talibijin, mataki ne mai amfani, na aiwatar da shirin hadin gwiwar al’adu tsakanin Sin da kasashen Afirka, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a taron kolin Johannesburg, na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC, wanda ya gudana a shekarar 2015. Ta ce matakin ya shaida dankon abokantakar gargajiya tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kuma Sin da Najeriya. 

A shekarun baya bayan nan, ana aiwatar da shirin taimakawa mazauna kauyukan kasashen Afirka samun damar kallon talibijin a kai a kai, matakin da ya baiwa duban-dubatar gidajen Najeriya damar kallon fina-finai da shirye-shiryen talabijin masu kayatarwa.

A nasu bangare, mazauna wurin nuna godiya suka yi da ziyarar jakadiya Yan, suna masu yabawa kamfanin Star Times, wanda da ya gudanar da aikin, na samar da hidimomin sanyawa, da kiyaye akwatunan talabijin masu amfani, da tauraron dan Adam masu inganci ga jama’a cikin dogon lokaci, ta yadda hakan ya taimaka musu wajen fahimtar duniya, da kuma gane al’adun Sin masu ban sha’awa. Mazauna kauyukan sun kuma bayyana Sin a matsayin abokiyar gaske ta al’ummun kasashen Afirka.  (Safiyah Ma)