logo

HAUSA

Jimilar kudin da Sin ta samu wajen jigilar kayayyaki a farkon watanni biyu na bana ta kai yuan triliyan 55.4

2024-03-29 12:44:25 CMG Hausa

Kungiyar tarayyar jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin, ta fitar da alkaluman gudanar da hada hadar jigilar kayayyaki daga watan Janairu zuwa Faburairun bana a yau Jumma’a. Inda aka nuna cewa, tun daga farkon bana, bukatun jigilar kayayyaki na Sin na samun farfadowa, kuma kasuwanni na ci gaba da habaka, yayin da saurin karuwar yawan jigilar kayayyaki ke kara karuwa.

Daga wannan Janairu zuwa Faburairu na bana, jimilar kudin da aka samu a fannin jigilar kayayyaki ta kai yuan triliyan 55.4, adadin da ya karu da kashi 5.9 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. Hakan dai ya shaida cewa, a halin yanzu gudummawar jigilar kayayyaki tana ta karuwa yadda ya kamata, sannan bukatun jigilar kayayyaki na ci gaba da habakawa.

Alkaluman sun nuna cewa, a fannin samar da hajojin masana’antu, sakamakon karuwar yawan kayayyakin da ake fitar da su zuwa ketare,  kaso 60 daga cikin kayayyakin masana’antu da ake samarwa sun samu karuwa, lamarin da ya aza harsashi mai inganci ga farfadowar aikin jigilar kayayyaki. (Safiyah Ma)