logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Kasa da kasa za su nuna shakku kan kudin da Japan za ta kashe don tsaron gida wanda ya kai matsayin koli a tarihi

2024-03-29 21:28:42 CMG Hausa

Rahotannin sun ruwaito cewa, kasar Japan ta zartas da kasafin kudinta na shekara ta 2024 a jiya Alhamis, ciki har da kudin tsaron gida na kudin kasar wato Yen tiriliyan 7.95, adadin da ya karu da kaso 16.9 bisa dari, wanda ya kai matsayin koli a tarihi.

Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian ya bayyana cewa, a ‘yan shekarun nan, Japan ta rika sauya manufofin tsaron gidanta, da kara kasafin kudi a wannan fanni, da sassauta kawo cikas ga fitar da makamai zuwa sauran kasashe, a wani yunkuri na neman raya karfin soja, al’amarin da zai jawo shakku daga kasashen Asiya dake makwabtaka da ita gami da sauran kasashen duniya, dake cewa, shin da gaske Japan tana tsayawa ga tsaron gida kawai, da neman bunkasuwa ta hanyar lumana?

Kaza lika, Lin Jian ya sanar a wanann rana cewa, bisa goron gayyatar da memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya ba shi, takwaransa na kasar Faransa Stephane Sejourne zai fara ziyara a kasar Sin tun daga ranar 1 ga watan Afrilu. Jami’in ya ce, a bana ake cika shekaru 60 da kulla huldar jakadanci tsakanin Sin da Faransa, kana, shekara ce ta sana’ar al’adu da yawon shakatawa tsakanin kasashen biyu. Ya ce kasar Sin na fatan yin kokari tare da Faransa, don zurfafa shawarwari kan batutuwan da suke jan hankalinsu dukka, da kara cimma nasarori a fannin hadin-gwiwa. (Murtala Zhang)