logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya ba da umarnin karawa wasu hafsoshin soji girma zuwa mukamin janar

2024-03-29 20:51:11 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma shugaban hukumar soji ta kasar, ya gabatar da takardun shaidar umarni na karin girma ga wasu hafsoshin soji biyu zuwa mukamin janar, a jiya Alhamis. Wannan shi ne mukami mafi girma ga hafsoshin soji dake bakin aiki a kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)