logo

HAUSA

Peng Liyuan ta gana da dalibai da malaman sakandaran Jamus dake Beijing

2024-03-29 10:04:34 CMG Hausa

Mai dakin shugaban kasar Sin Peng Liyuan ta gana da wakilan dalibai da malaman wata makarantar sakandaran kasar Jamus dake birnin Beijing a jiya Alhamis. Makarantar dai na koyar da dalibai salon rera wakokin majami’a da harshen Sinanci, kuma yayin ganawarta da wakilan daliban, Peng ta taya su murnar cimma tarin nasarori cikin shekaru 10 da suka gaba, a fannin yaukaka kawance ta hanyar rera wakoki.

Uwargida Peng ta kara da cewa, ta hanyar gudummawar kowa, kungiyar ’yan makarantar ta rera wakoki, ta gina wata gadar musayar al’adu tsakanin Sin da Jamus, ta kuma zama muhimmiyar alamar kawance tsakanin Sin da Jamus. (Saminu Alhassan)