logo

HAUSA

Kasar Sin na gaggauta matakai a bangaren kirkirowa da mallakar fasaha mai inganci

2024-03-29 16:01:50 CGTN HAUSA

Hukumar lura da ikon mallakar fasaha ta kasar Sin, ta kira wani taron manema labarai a yau Juma’a, inda ta yi bayani kan yadda ake kiyayewa, da tabbatar da tsare-tsare a bangaren ikon mallakar fasaha, a wa’adin babban shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki, da zamantakewar kasar Sin na 14.

Bisa sabbin alkaluman da aka bayar, an ce an cimma nasarar aiwatar da shirin da aka tsara, musamman ma a wasu bangarori hudu, ciki hadda darajar ikon mallakar fasaha da aka yiwa rajista, da yawan kudaden da aka kashe wajen samun ikon mallakar fasaha a cikin gida da na waje, da amincewar al’umma wajen kiyaye ikon, kana da amincewar al’umma a bangaren hukuncin da kotuna suka yanke game da kararrakin da aka gabatar musu a wannan fanni.

Ban da wannan kuma, a wasu bangarori 2, an samu ci gaba fiye da kiyasin da aka yi, wato yawan ikon da aka mallaka kan duk mutane dubu 10, da karuwar bangaren sana’o’i masu bukatar dimbin ikon mallakar fasaha a bisa yawan GDPn kasar.

Ya zuwa karshen shekarar 2023, a babban yankin kasar Sin, wato ban da yankin Hongkong, da Macao da Taiwan, yawan ingantattun fasahohin da aka mallaka ya kai miliyan 1 da dubu 665. (Amina Xu)