logo

HAUSA

Sin za ta kara bunkasa alaka da kungiyar kasashen Larabawa

2024-03-29 10:26:40 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya gana da sabon shugaban ofishin wakilci na kungiyar kasashen Laraba ta AL na kasar Sin Ahmed Mustafa Fahmy. Yayin ganawar tasu jiya a birnin Beijing, jami’an biyu sun alkawarta yin aiki tare, domin bunkasa alakar Sin da kasashen Larabawa.

Wang ya ce dangantakar Sin da kasashen Larabawa na cikin yanayi mafi kyau a tarihi, kuma Sin a shirye take ta yi aiki tare da kungiyar AL, wajen aiwatar da manufofin da shugabannin sassan biyu suka amincewa, tare da ingiza gina al’ummar Sin da kasashen Larabawa mai makomar bai daya.

A nasa bangare kuwa, Fahmy cewa ya yi bangaren Larabawa na jinjinawa matsayar adalci ta Sin game da batun Falasdinawa, da goyon bayanta ga kasashen Larabawa, don haka zai yi iyakacin kokari, wajen bunkasa dangantakar kasashen Laraba da kasar ta Sin. (Saminu Alhassan)