logo

HAUSA

Sama da fursunoni 100 ke jiran afuwa daga gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya

2024-03-29 09:40:46 CMG Hausa

A kalla sama da daurarru 100 ne da aka yankewa hukuncin kisa suke jiran neman afuwa daga gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya, wanda kuma suke ci gaba da zama a gidajen gyaran halin dake sassan jihar.

Babban jami’in hukumar mai lura da jihar ta Kano Alhaji Sulaiman M. Inuwa ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake gabatar da sunayen mutanen ga kwamitin yi wa fursunoni afuwa da gwamnatin jihar Kano ta kafa. Ya ce, wannan adadi yana karuwa ne lokaci zuwa lokaci saboda yawan zartar da hukunce-hukuncen kisa da kotunan jihar ke yi lamarin dake haifar da cunkoso a gidajen yarin.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Kwamitin wanda ke karkashin jagorancin Hajiya Azumi Namadi Bebeji sun ziyarci babban gidan yari na zamani da aka gina a garin Janguza dake jihar ta Kano da nufin duba halin da daurarrun ke ciki tare da nazari a kan wadanda suka dace a yi wa afuwa daga cikin masu laifin da aka yankewa hukuncin kisa.

Da yake yiwa manema labarai karin haske a game da ziyarar a madadin shugaban hukumar, jami’in yada labarum hukumar Alhaji Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya ce a yanzu haka akwai mutanen da suka shafe shekaru 25 zuwa 30 har yau kuma ba su san matsayinsu ba.

“Da wahala a dauki wata daya ba ka ji an ce an yankewa mutum hukuncin kisa ba, kuma karuwa suke yi ba wai raguwa suke ba, mshi ye sa utum biyu ne kawai suke da ikon sallamar duk wanda ya samu kansa a irin wannan hali, na farko shugaban kasa, na biyu gwamna, ko kuma mutum ya yi daukaka kara wanda yin hakan zai iya rushe hukuncin farko, to amma mu matsalar da muka samu a nan arewacin Najeriya shi ne ba mu da wayewar yin Appeal zuwa kotu ta gaba.”

Daga karshe shugabar kwamitin ta tabbatarwa hukumar cewa, za ta gabatarwa gwamna dukkannin bukatunsu, sannan kuma ta yaba matuka bisa yadda ta ga mutanen da ake tsare da su, suka himmatu sosai wajen neman ilimin addini da na zamani. (Garba Abdullahi Bagwai)