logo

HAUSA

Manyan daraktocin kamfanonin ketare sun amince da makomar kasuwar kasar Sin

2024-03-28 16:27:55 CGTN HAUSA

 

Da yammacin yau Alhamis a gun wani taron manema labarai, mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin He Yadong, ya yi tsokaci game da ziyarar da wasu manyan daraktocin kamfanonin ketare suka yi a nan kasar Sin a kwanan baya.

He Yadong ya nuna cewa, shugabannin ma’aikatar sun gana da manyan daraktocin kamfanoni fiye da 20, ciki hadda Apple, da Qualcomm, da Mercedes Benz da sauransu. A takaice dai, kamfanonin na da kwarin gwiwa a fannin zuba jari a nan kasar Sin. An ce, daga watan Jarairu zuwa Fabrairu, yawan karin kamfanonin ketare da su kafa sassansu a nan kasar Sin ya karu da kashi 34.9%, matakin da ya shaidu ikirarin jami’in na Sin.

Yayin da aka tabo batu kan karar da Sin ta gabatarwa WTO, kan manufar da Amurka ke dauka, ta hana kamfanonin Amurka da su sayi sassan batir daga kasar Sin. He Yadong ya yi nuni da cewa, Amurka na nunawa kasar Sin banbanci a manufar ba da rangwame bisa hujjar tinkarar sauyin yanayi, da hana fitar da hayaki mai dumaman yanayi, wanda hakan ya gurgunta halin takara bisa adalci, da ma tsarin samarwa, da jigilar motoci masu aiki da sabbin makamashi a duniya. (Amina Xu)