logo

HAUSA

Shugaban zaunannen kwamitin NPC na Sin ya gana da jami’ai a dandalin Boao

2024-03-28 11:34:51 CMG Hausa

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC Zhao Leji, ya gana da ’yan kwamitin gudanarwa na dandalin Boao na nahiyar Asiya ko BFA, da wasu daga wakilan majalissar bayar da shawarwari ta taron, da kuma wasu muhimman abokan huldar taron na Boao.

Yayin ganawar da ta gudana a Boao na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin a jiya Laraba, Zhao Leji ya ce taken dandalin na bana, wato "Asiya da duniya: kalubalen bai daya, da nauyaye-nauyaye kowa da kowa", ya mayar da hankali ga shawo kan batutuwa dake jan hankulan sassan kasa da kasa, wanda hakan ke da muhimmanci a zahiri.

Ya ce a duniyar yau, kalubale daban daban, da rikice-rikice sun sarke da juna, to amma duk da haka, yayin da ake fuskantar kara tsanantar al’amura, haka kuma ya dace a kara azamar cimma daidaito, da goyon bayan juna da hadin gwiwa.

Zhao Leji ya kara da cewa, "Sin za ta samarwa duniya karin damammaki karkashin gajiyar sabbin sassan ci gabanta, kana za ta ci gaba da goyon bayan bunkasar dandalin na BFA. Daga nan sai ya yi fatan cewa, dandalin zai ba da babbar gudummawa ga wanzar da zaman lafiya, da ci gaban nahiyar Asiya da ma sauran sassan duniya baki daya. (Saminu Alhassan)