logo

HAUSA

Tsohon firaministan Japan: Ana sa ran Sin za ta taka rawar gani wajen ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai dorewa

2024-03-28 15:18:44 CGTN HAUSA

Jiya Laraba, tsohon firaministan kasar Japan Fukuda Yasuo, ya shaidawa manema labarai na CMG cewa, tattalin arzikin Sin na kawo babban tasiri ga na sauran duniya. Yasuo ya yi fatan Sin za ta yi kokarin bunkasa tattalin arzikinta, don ci gaba da taka rawar gani ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai dorewa.

Kaza lika, tsohon firaministan ya yaba da tsarin da Sin take aiwatarwa na raya sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko, kuma yana mai fatan sabbin abubuwan kimiyya da Sin ta kirkiro, za su taimakawa duniya a bangaren shimfida zaman lafiya mai karko. Ya ce, “matakin ya bayyana aihinin ma’anar kafa makomar Bil Adama ta bai daya.”

(Amina Xu)