logo

HAUSA

Kasar Sin ta soki takalarta da Philippines ke yi da katsalandan din Amurka dangane da batun tekun kudancin Sin

2024-03-28 20:18:43 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da tsaron kasar Sin ta bayyana a yau Alhamis cewa, kasar ba za ta kyale Philippines ta yi abun da ta ga dama dangane da batun tekun kudancin Sin ba, kuma ta na adawa da katsalandan din Amurka.

Yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, kakakin ma’aikatar Wu Qian, ya ce babu wani abu dake haifar da rikici a yankin face katsalandan din Amurka. Haka kuma, takala da tsokana da Philippines ke yi, su ne ke ta’azzara batun a baya-bayan nan.

Ya kara da cewa, kasar Sin na adawa da katsalandan daga kasashen waje da takala da keta doka dangane da batun tekun kudancin kasar dake tsakaninta da Philippines, haka kuma tana kira da a warware sabanin ta hanyar da ta dace.

Bugu da kari, Wu Qian ya ce kasar Sin na cikin shirin ko-ta-kwana, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare yankuna da ‘yanci da halallattun hakkoki da muradunta na teku. (Fa’iza Mustapha)