logo

HAUSA

Kasar Sin na nuna cikakken goyon-baya ga Pakistan wajen yakar ta’addanci

2024-03-28 20:34:05 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Lin Jian, ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasarsa ta nuna godiya ga jawabin shugaban kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya na tir da harin ta’addancin da aka kai wa Pakistan, jawabin da ya shaida babbar aniyar kasa da kasa wajen yakar ta’addanci. Kaza lika, kasar Sin tana adawa da duk wani yunkuri na aikata ta’addanci, da mara wa Pakistan baya wajen daukar matakan murkushe ayyukan ta’addanci.

Rahotannin da aka ruwaito sun ce, kwamitin sulhun MDD ya fitar da jawabin shugabansa a jiya Laraba, inda ya yi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a yankin Besham dake lardin Khyber Pakhtunkhwa na kasar Pakistan.

Bugu da kari, a yayin da yake amsa tambayar da ta shafi martaninsa kan furucin ministan harkokin wajen New Zealand, Lin Jian ya ce, kamar sauran kasashe masu rungumar zaman lafiya, kasar Sin ita ma tana damuwa matuka kan dangantakar AUKUS dake tsakanin kasashen Amurka da Birtaniya da kuma Australiya, wato wai “dangantakar abuta ta fuskar tsaro tsakanin bangarorin uku”, inda ta bayyana fatanta na ganin cewa, bangarori masu ruwa da tsaki za su kara aikata abubuwan alheri don taimakawa samun fahimtar juna da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. (Murtala Zhang)