logo

HAUSA

Sin na amfani da kimiyya da fasaha wajen kiyaye muhalli

2024-03-28 11:19:53 CGTN HAUSA

Jiya Laraba, hukumar kare muhalli ta kasar Sin ta kira wani taron manema labarai, inda aka nuna cewa, hukumar na mai da hankali matuka wajen fitar da muhimmiyar kimiyya da fasaha dake da nasaba da muhalli, kuma ta gudanar da manyan ayyuka kimiyya da fasaha, lamarin da ya magance wasu matsalolin muhalli.

Wani jami’in hukumar ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, Sin ta kafa muhimman dakunan gwaji 40, da cibiyoyin fasahar ayyuka 38, da tasoshin nazarin kimiyya 7, wadanda suke mai da hankali kan bangarorin ruwa, da iska, da kasa, da muhalli, da tsaron nukiliya da sauransu.

A cikin wadannan ayyukun, an fitar da dalilin gurbacewar iska mai tsanani da dabarar magance ta, daga cikin dabarun akwai muhimmiyar fasahar kimantawa, da tsara manufofi da dai sauransu. Haka kuma, an kirkiri fasahar magance gurbacewar ruwa daga asali, da kyautata muhallin tabki, da kogi, da ta sa ido da kandagarki, da kuma tabbatar da ingancin ruwan sha, da dai sauran fasahohi.

Kaza lika, tsarin kiyaye muhallin kogin Yantse, ya sa a yi bincike kan dalilan dake haifar da muhimman matsalolin da kogin ke fuskanta, da fitar da dabarun magance su yadda ya kamata.  (Amina Xu)