logo

HAUSA

Sin ta yi tir da harin ta'addanci a Pakistan tare da kira da a gudanar da cikakken bincike

2024-03-27 10:23:45 CMG Hausa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce Sin ta yi matukar Allah wadai da harin bam da ya auku a Dasu na kasar Pakistan, tana kuma fatan za a gaggauta gudanar da cikakken bincike game da hakan.

Kakakin wanda ya bayyana matsayar kasar Sin don gane da harin na ta'addanci, ya ce da karfe 1 na tsakar ranar jiya Talata, Sinawa 5, da dan kasar Pakistan 1 sun rasa rayukansu, sakamakon harin da aka kaiwa jerin gwanon motocin su, a kan hanyar su ta zuwa tashar samar da lantarki ta Dasu da kamfanin kasar Sin ke ginawa a lardin Khyber Pakhtunkhwa.

Jami'in ya kara da cewa, Sin na matukar Allah wadai da wannan aiki na ta'addanci. Tana kuma mika sakon ta'aziyya da jaje ga iyalan wadanda harin ya ritsa da su. Kaza lika, Sin ta bukaci Pakistan da ta gaggauta gudanar da cikakken bincike, ta farauto wadanda suka aikata laifin, kana ta gurfanar da su gaban shari'a.

A daya bangaren, Sin na fatan Pakistan za ta dauki sahihan matakai na tabbatar da tsaron Sinawa, da wuraren ayyukan su, da cibiyoyin Sin dake kasar. Bugu da kari, Sin na aiki tare da Pakistan wajen ganin an tantance halin da ake ciki daga dukkanin fannoni. (Saminu Alhassan)