logo

HAUSA

Xi Jinping: ya kamata bangarori daban daban na Sin da Amurka su kara mu’amala da fahimtar juna

2024-03-27 17:23:04 CMG Hausa

A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan bangarorin masana’antu da kasuwa da ilmi na kasar Amurka a babban dakin taron jama’ar kasar Sin dake nan birin Beijing.

A yayin ganawar, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, tarihin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, tarihi ne na sada zumunta a tsakanin jama’ar kasashen biyu, kuma ana bukatar jama’ar kasashen biyu su rubuta tarihin tare, tun a zamani baya har zuwa nan gaba. Shugaban ya kuma yi fatan wakilan bangarori daban daban na kasashen biyu za su kara mu’amala da fahimtar juna. (Zainab Zhang)