logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya jajanta harin ta’addancin da aka kai wa Rasha

2024-03-27 20:03:38 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya rubuta sako a jiya Talata, cikin wani littafin jaje da ofishin jakadancin Rasha ya bude dangane da harin ta’addancin da aka kai Moscow.

Cikin sakon, Wang Yi ya jajantawa wadanda harin ya rutsa da su, yana mai cewa, kasar Sin na adawa da dukkan nau’ikan ta’addanci, kuma tana tir da harin, kana tana mara baya ga kokarin gwamnatin Rasha na kare tsaro da zaman lafiya a kasar.

Mutane da yawansu ya kai 139 ne suka mutu sanadiyyar harin da aka kai wani zauren kide-kide dake kusa da birnin Moscow a ranar 22 ga wata, wanda ya kasance harin ta’addanci mafi muni da Rasha ta gani cikin shekaru da dama. (Fa’iza Mustapha)