logo

HAUSA

Babban bankin Najeriya ya kara kudin ruwa zuwa kaso 24.75 bisa dari

2024-03-27 10:48:04 CMG Hausa

Babban bankin Najeriya CBN, ya kara kudin ruwa zuwa kaso 24.75 bisa dari, wato karin maki 200 kan na baya, a gabar da kasar mafi yawan al’umma a Afirka ke fuskantar hauhawar farashin kayayyaki.

Gwamnan babban bankin Najeriya Yemi Cardoso, wanda ya jagoranci zaman kwamitin tsara manufofin kudi da ya gudana jiya Talata a birnin Abuja fadar mulkin kasar, ya shaidawa manema labarai a karshen zaman cewa matakin na CBN, ya biyo bayan karin da aka yi a watan da ya gabata, inda a wancan lokacin aka kara kudin ruwan zuwa kaso 22.75 bisa dari.

Matakin dai yana da alaka da matsin hauhawar farashin kayayyaki, da bukatar dakile hasashen karuwar hauhawar farashin kayayyakin, da kuma tabbatar da daidaito a farashin musayar kudaden waje.

A cewar mista Cardoso, mambobin kwamitin sun yi imanin cewa, ci gaba da karuwar kudin ruwa na da nasaba da hauhawar farashin kayayyakin abinci saboda karancin su a kasuwanni, da tsadar hada hadar sufuri da rarraba su. Don haka kwamitin na ganin shawo kan karancin abinci, shi ne jigon magance matsin hauhawar farashin kayayyakin abinci.

A watan Fabarairu da ya gabata, mizanin hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu daga kaso 29.90 zuwa 31.70 bisa dari, sakamakon karuwar farashin abinci, kamar dai yadda alkaluman hukumar kididdiga ta kasar NBS suka tabbatar. (Saminu Alhassan)