logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da baki Amurkawa bi da bi

2024-03-27 11:09:02 CMG Hausa

Mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da shugaban hukumar manyan shugabannin zartaswa na kwamitin kasar Amurka mai lura da dangantakar Amurka da Sin Evan Greenberg, da shugaban kwamitin Steve Orlins, da kuma farfesa Graham Allison na jami’ar Harvard bi da bi a birnin Bejing.

Yayin ganawarsa da Evan Greenberg, da Steve Orlins, Wang Yi ya jadadda cewa, matsalar dake tsakanin dangantakar Sin da Amurka ita ce bangaren Amurka ya dauki Sin a matsayin abokiyar takararta mafi girma, da kasancewa kalubalen siyasarta mafi girma, irin wannan fahimta ta kuskure ta haddasa matsaloli ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ya ce kamata ya yi bangaren Amurka ya yi tafiya a kan hanya guda tare da Sin, ta yadda za a iya inganta dangantakar kasashen biyu wajen samun daidaito, da kyautatuwa da kuma ci gaba.

Bangaren Amurka ya bayyana cewa, ci gaba da mu’ammala da juna, da tabbatar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, zai haifar da ci gaba a kan hanya mai dacewa, zai kuma samar da alheri ga duk fadin duniya. Kaza lika kwamitin kasar Amurka na dangantakar Amurka da Sin, yana fatan a samu ci gaba, da ba da gudummawa ga mu’ammalar kasashen biyu.

Yayin ganawarsa da Graham Allison kuwa, Wang Yi ya ce ya kamata Sin da Amurka su tinkari kalubalolin kasa da kasa tare, ta yadda za a gina dangantaka cikin kwanciyar hankali da dorewa.

Allison ya bayyana cewa, dole ne Amurka da Sin su yi hadin gwiwa, dole ne su samu hanya mai dacewa ta kulla huldarsu. Har ila yau, ya yi fatan kara fahimtar manufar diplomassiyar Sin ta hanyar fahimtar tarihi, da al’adu masu zurfi na kasar. (Safiyah Ma)