logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya amince da kafa asusun musamman don samar da ababen more rayuwa a kasa

2024-03-26 08:54:32 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa asusun musamman da zai mayar da hankali wajen samar da ababen more rayuwa ga al’umma, a wani mataki na cike gibin dala miliyan 25 da ake samu a kowacce shekara cikin kasafin kudin kasar wajen tafiyar da ayyukan raya kasa.

Shugaban ya amince da kafa asusun ne jiya Lititin 25 ga wata yayin taron majalissar zartaswar kasar wanda ya jagoranta a fadarsa dake birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

A lokacin da yake karin haske ga ’yan jaridu a kan al’amarin jim kadan da kammala taron, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na tarayyar Najeriya Alhaji Muhammad Idirs ya ce, asusun idan an kaddamar da shi zai kasance ne karkashin kulawar fadar shugaban kasa.

Ministan yada labaran ya ci gaba da cewa, daga cikin muhimman bangarorin da za a yi amfani da kudin asusun wajen raya su, sun hada da batun samar da titunan mota da na jirgin kasa, bunkasa sha’anin noma, da bunkasa harkokin tasoshin jiragen ruwa da kuma harkokin sufurin jiragen sama.

Alhaji Muhammad Idris ya ce, kafin a kai ga yanke shawarar assasa wannan asusun an gudanar da Nazari ne sosai, inda daga bisani aka tabbatar da cewa, muddin Najeriya na son cike gibin karancin ayyukan raya kasa, wajibi ne dai ta samar da karin dala biliyan 875 a bangaren a tsakanin shekara ta 2016 zuwa shekara ta 2040 wannan ya nuna cewa, a duk shekara za a rinka kashe dala biliyan 35 wajen gina tituna, asibitoci, kyautata sha’anin sadarwa tare kuma da farfado da ayyukan masana’antu.

“Hakika wannan wata dabara ce shugaban kasa ya gabatarwa gwamnatin tarayya domin dai tabbatar da ganin cewa Najeriya tana da yalwataccen kayayyakin more rayuwa.”

Nan da ’yan watanni ne dai za a kaddamar da asusun bayan ministan tsare-tsaren tattalin arzikin kasar ya shirya wani kwarya-kwaryar kasafin kudi da zai kunshi bukatun sabon asusun. (Garba Abdullahi Bagwai)