logo

HAUSA

Ana sa ran dandalin Boao na bana zai hallara mutane kimanin 2,000

2024-03-26 15:33:45 CMG Hausa

Babban sakataren taron shekara-shekara na dandanlin kasashen Asiya na Boao, ko BFA a takaice Li Baodong, ya ce ana sa ran taron na bana zai hallara kimanin mutane 2,000.

Li, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na farko da aka gudanar domin dandalin a yau Talata. Ya ce taron Boao na 2024, zai gudana ne tun daga yau Talata zuwa Juma’a 29 ga watan nan na Maris, a Boao na bakin teku dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin.

Ya ce a bana dandalin zai hallara wakilai kusan 2,000 daga sama da kasashe da yankuna 60, baya ga ’yan jarida sama da 1,100 da za su halarta daga kusan kasashe da yankuna 40.

Taken dandalin na wannan karo shi ne "Asiya da duniya: kalubalen bai daya, da nauyin dake wuyansu". Kaza lika, ana sa ran dandalin zai mayar da hankali ga muhimman batutuwa guda biyar, wato "Tattalin arzikin duniya, da kirkire kirkiren kimiyya da fasaha, da ci gaban zamantakewar al’umma, da hadin gwiwar kasa da kasa, da batun tunkarar kalubaloli tare”.   (Saminu Alhassan)