logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin da ta Honduras sun taya juna murnar cika shekara daya da kulla huldar diplomasiyya

2024-03-26 10:04:39 CGTN HAUSA

 

A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwararsa ta kasar Honduras Iris Xiomara Castro Sarmiento, suka taya juna murnar cika shekara daya da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen su. 

Yayin zantawar da shugabannin biyu suka yi ta wayar tarho, shugaba Xi ya ce a watan Maris din shekarar bara, Sin da Honduras suka kulla dangantakar diplomasiyya, inda aka bude sabon babin huldarsu. Abubuwan da suka faru a cikin shekara daya da ta gabata, sun shaida cewa kullawar huldar ta dace da halin da ake ciki, ta kasance nagartaccen matakin siyasa, kuma ta dace da muradun kasashen biyu da al’umomminsu.

A nata bangare, Iris Xiomara Castro Sarmiento ta yi nuni da cewa, har kullum Honduras na nacewa ka’idar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, tana kuma fatan raya huldarsu bisa tushen dogaro da mutunta juna. (Amina Xu)