logo

HAUSA

Kasar Sin na maraba da kudurin da Kwamitin Sulhu ya zartar dangane da tsagaita wuta a Gaza

2024-03-26 19:55:43 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau cewa, kasar na maraba da kudurin da Kwamitin Sulhu na MDD ya zartar, wanda ke bukatar tsagaita bude wuta nan take a Gaza.

Rahotanni sun ruwaito cewa, kudurin wanda ya samu kuri’un amincewa 14 daga mambobin kwamitin 15, shi ne irinsa na farko da kwamitin ya zartar tun bayan barkewar rikici tsakanin Isra’ila da Palasdinu a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ke neman tsagaita wuta a Gaza.

Da yake tsokaci game da kudurin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce zartar da kudurin ya dace da ayyukan kwamitin da kuma abun da daukacin al’ummun kasa da kasa ke sa ran gani.

Ya kara da cewa, kasar Sin na sa ran kasashe masu tasiri za su taka rawar da ta dace ga dukkan bangarori, ciki har da amfani da dukkan matakan da suka dace kuma suka wajaba, wajen mara baya ga aiwatar da kudurin. (Fa’iza Mustpha)