logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Zuba jari a Sin zai taimaka wajen samun nasara a nan gaba

2024-03-26 20:58:33 CMG Hausa

A yayin taron dandalin tattaunawa kan ci gaban kasar Sin na shekarar 2024 da aka kammala ba da dadewa ba, shugabannin kamfanonin kasa da kasa kusan 100 da suka hada da Apple Inc. da ke Amurka, da bankin HSBC na kasar Birtaniya, da kamfanin Mercedes Benz da ke kasar Jamus, sun hallara a nan birnin Beijing, inda suka tattauna kan kara zuba jari a kasar Sin. Game da haka, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau Talata 26 ga wata, a gun taron manema labaru da aka saba yi cewa, tafiya da kasar Sin na nufin tafiya da damammaki, kuma zuba jari a kasar zai taimaka wajen samun nasara a nan gaba.

Baya ga haka kuma, a ranar 26 ga watan Maris din bana ne aka cika shekara 1 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Honduras. Game da wannan batun, Lin Jian ya bayyana cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya shekara guda da ta wuce, kasashen Sin da Honduras, suna goyon bayan juna kan batutuwan da suka shafi muhimman muradunsu, kuma sun gudanar da hadin gwiwa mai inganci a fannoni daban daban kamar tattalin arziki da cinikayya, da aikin gona, da kimiyya da fasaha, da ba da ilimi, da yawon bude ido da dai sauransu, lamarin dake nuna fa’idoji masu tarin yawa, dake nuna kyakkyawar makoma a nan gaba. A cewar kakakin, saurin ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Honduras ya tabbatar da cewa, kulla dangantaka da kasar Sin bisa manufar Sin daya tak, yana dacewa da yanayin tarihi da na zamani gaba daya, da ma muhimman muradun kasashen biyu, da jama’arsu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)