logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Nauru

2024-03-25 19:56:45 CMG Hausa

Da yammacin yau Litinin 25 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Nauru, David Ranibok Adeang, wanda yanzu haka ke ziyara a kasar Sin, a babban dakin taron jama’a.

Kafin shawarwarin kuma, shugaba Xi ya shirya bikin maraba ga shugaba Adeang.

Bisa gayyatar da shugaba Xi ya yi masa ne, shugaba Adeang yake ziyarar aiki a kasar ta Sin daga ranar 24 zuwa 29 ga wata. (Mai fassara: Bilkisu Xin)