logo

HAUSA

An kaddamar da cibiyar yada labarai ta dandalin Bo’ao

2024-03-25 10:12:38 CGTN HAUSA

 

Za a gudanar da dandalin Bo’ao na nahiyar Asiya daga gobe Talata zuwa ranar Juma’a 29 ga watan da muke ciki, a garin Bo’ao na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.

Taken dandalin na bana shi ne “Asiya da duniya: Fuskantar da kalubaloli da sauke nauyin bai daya”. Za a kebe bangarorin tattaunawa hudu, wato na tattalin arzikin duniya, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da bunkasuwar al’umma, da kuma hadin gwiwar kasa da kasa, kuma a karkashinsu, za a gabatar da kananan bukukuwan tattaunawa fiye da 40.

Da yammacin yau Litinin ne za a kaddamar da cibiyar yada labarai ta dandalin, inda tuni aka shirya tsaf don gudanar da shi. (Amina Xu)