logo

HAUSA

Shugaban NPC zai halarci taron dandalin Boao na 2024

2024-03-25 20:16:32 CMG Hausa

Bisa gayyatarsa da aka yi, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji, zai halarci bikin bude taron shekara-shekara na dandanlin kasashen Asiya na Boao na bana da za a yi a Hainan.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ne ya bayyana haka a yau Litinin, inda ya ce Zhao Leji zai kuma gabatar da jawabi ga taron dandalin a ranar 28 ga wata. (Fa’iza Mustapha)