logo

HAUSA

Tauraron dan adam na Queqiao-2 ya shiga falakinsa a zagayen wata

2024-03-25 20:19:08 CMG Hausa

Hukumar kula da harkokin sama jannati na kasar Sin, ta ce tauraron dan adam na kasar wato Queqiao-2, ya yi nasarar tsayawa kusa da wata, inda ya shiga falakinsa a zagayen watan.

Ta hanyar daidaita tsawonsa da tudunsa, tauraron Queqiao-2 zai shiga falakinsa a zagayen wata kamar yadda aka tsara, tare da aiwatar da gwaje-gwajen sadarwa da kumbunan binciken wata na Chang’e-4 da Chang’e-6 kamar yadda aka tsara. (Fa’iza Mustapha)