logo

HAUSA

Peng Liyuan ta yi rangadin aikin rigakafi da shawo kan cutar tarin fuka a birnin Changsha na lardin Hunan

2024-03-24 16:59:04 CMG Hausa

Jakadiya mai isar da alheri ta kungiyar WHO mai kula da rigakafin cututtukan tarin fuka da AIDS, kana uwargidan shugaban kasar Sin, madam Peng Liyuan, ta yi rangadi kan yadda ake gudanar da aikin rigakafi da shawo kan cutar tarin fuka a titin Dongjing da ke yankin Yuhua a birnin Changsha na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin.

Ranar 24 ga watan Maris, ita ce ranar yaki da cutar tarin fuka karo na 29 a duniya.

Peng Liyuan da tawagarta sun fara zuwa cibiyar fadakar da al’umma kan ilimin kiwon lafiya dake yankin Yuhua, domin sauraron yadda ake gudanar da ayyukan koyar da ilmin kiwon lafiya a wurin, da kara fahimtar yadda ake gina tsarin rigakafi da shawo kan cutar tarin fuka, inda ta yi kira ga mutanen wurin da su yi aiki a matsayin masu wayar da kai da kuma sa kai, don karfafa yada ilmin rigakafi da shawo kan cutar tarin fuka a tsakanin mazauna da matasa a unguwanni yadda ya kamata.

A cibiyar kula da lafiyar al'umma ta titin Dongjing kuwa, Peng Liyuan ta ziyarta tare da gaida ma'aikatan kiwon lafiya na wurin, da fahimtar yadda ake gudanar da ayyukan jinyar cutar tarin fuka. Baya ga haka, ta tattauna sosai da masu fama da cutar tarin fuka wadanda suka je neman shawarwarin lafiya, da ma yara masu jiran rigakafin da iyayensu. Ta kuma bayyana fatan kowa zai ci gaba da ba da gudunmawa wajen kawo karshen annobar ta tarin fuka. (Mai fassara: Bilkisu Xin)