logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya bukaci al`ummar kasar da su rungumi akidar amfani da kayan da ake samarwa a gida

2024-03-24 16:14:51 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al`ummar kasar da su mayar da hankali wajen amfani da kayayyakin da ake samarwa a cikin kasar maimakon dogaro da na kasashen ketare.

Mashawarcin shugaban da ke kula da harkokin yada labarai Mr Ajuri Ngelale ne ya bukaci hakan a madadin shugaban lokacin da yake ganawa da manema labaran fadar shugaban kasa, ya ce kiran ya zama wajibi domin taimakawa kokarin gwamnati na farfado da darajar Naira.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Mai magana da yawun shugaban na tarayyar Najeriya ya tabbatar da cewa yanzu haka gwamnati na dauka managartan matakai domin rage mummunan tasiri da kudaden kasashen wajen ke yi a kan naira.

Ya ce daya daga cikin irin wadannan matakai shi ne mayar da hankali wajen amfani da kayayyakin da ake samarwa a cikin gida, inda ya ce babu yadda za a yi a samu bunkasuwar tattalin arziki a cikin gida a lokacin da hankalin al`ummar kasa ya karkata kan sha`awar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje.

Mr Ajuri ya ce domin karfafa gwiwar kananan da matsakaitan masana`antu na cikin gida, gwamnatin tarayya ta bullo da shirye-shiryen tallafin kudin domin karfafa jarin irin wadannan masana`antu. , shirye shiryen da suka hada da.

“Shirin bayar da tallafin kudi da shugaban kasa ya bullo da shi wanda sama da `yan kasuwa `yan Najeriya miliyan da ya za su amfana da kyautar naira dubu hamsin domin su habaka kananan sana’o’in da suke yi.”

Haka kuma mai magana da yawun shugaban na tarayyar Najeriya Mr Ajuri Ngelale ya ce gwamnati ta rabar da bashi mai rangwamen kudin ruwa da ya kai na sama da naira biliyan 150 ta hannun bankin masana`antu da kuma hukumar SMEDAN ga masu kananan da matsakaitan masana`antu su dubu dari dake daukacin kananan hukumomin kasar, duk dai domin karfafa gwiwar samar da kayyyakin bukatun yau da kullum a cikin gida .(Garba Abdullahi Bagwai)